|
Me ake nufi da mu'ujizar ilimi?
Mu'ujizar ilimi fuskaci ne na fuskokin mu'ujzar
Alqur'ani da Sunna kuma sun qunshi:-
-
mu'ujizar bayani da lugga.
-
Mu'ujizar labarai(tarihi).
-
Mu'ujizar shari'a.
-
Mu'ujizar ilimi(kimiya).
mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi wani reshe ne
na fassarar kimiyya da Alqur'ani da Sunna suka yi nuni
garesu,nuni kuma abayyane acikin nassi ,gwargwadon yadda
qa'idojin ilimi suka tabbatar , kuma waxannan abubuwa
an tabbatar da cewa ba za a iya ganosu ba a zamanin
manzo (s.a.w), abinda ke qara tabbatar da gaskiyar
manzancin manzo(s.a.w) na game da abinda ya bada
labarinsa daga Allah (s.w).
kafa wannan qungiya da bunqasata:
-
a shekara ta 1404 aka kafa wannan qungiya ta mu'ujizar
Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi da izini daga babban
majalisa ta masallatai ta duniya ataronsu na tara.
-
A shekara ta 1406 hijiriyya, babban majalisar ta amince
da kafa wannan qungiya ta mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a
fagen ilimi, kuma babban sakatarenta shine Sheik
Abdulmajid Alzindani.. sannan qungiyar ta zavi qungiyar
qasashen musulmi ta duniya dake Maka ta zama cibiyarta,
kuma ta buxe rassanta acikin Saudiyya da wajenta don
cimma burinta..
-
A shekara ta 1423 kwamitin zartarwa ta qungiyar
qasashen musulmi a zamanta na 38 ta amince da bunqasa
qungiyar aka sa mata suna: qungiya ta mu'ujizar
Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi ta zamo daya daga cikin
kwamitocin qungiyar qasashen musulmi ta duniya mai zaman
kanta, kamar haka :
-
qungiyar ta haxa majalisar qungiyar- kwamitin zartarwa-
Babban sakatare.
-
Dokta Abdallah Muslih ya riqe maqamin babban sakatare a
shekara ta 1423 har ya zuwa yanzu.
Manufofin qungiyar:
Kungiyar tana aiki don cimma manufofi kamar haka:
-
Sanya kai'doji da dokoki da zasu tantance ijtihadi
acikin mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi.
-
Bayyanar da voyayyun ma'anonin ayoyin alqur'ani da
hadisan manzo(s.a.w) waxanda suke da alaqa da ilimin
yanayin duniya, acikin hasken tafsiri da abinda lugga ya
tabbatar da manufofin shari'ar musulumci ba tare da
matsawa ba.
-haxa ilimi kauni da haqiqar imani da shigar da abinda
binciken ya cimma a manhajar koyarwa a dukkan kafafe.
- taimakawa wurin samar da manazarta da malamai don
binciken ilimi da haqiqar duniya acikin abin da yazo a
Alqur'ani da Sunna.
- fuskantar da mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen
ilimi don ta zama hanyar da'awa..
-haxa qoqarin da akayi a duniya a fagen mu'ujizar
Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi.
Qungiyar tana amfani da hanyoyi da suka dace da
shari'ar musulumci daga ciki:
1.
sanya ma'aunin binciken mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a
fagen ilimi.
2.
nazarin ayoyi da hadisai da suke da dangantaka da
mu'ujizar ilimi.
3.
nazarin binciken mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen
ilimi, da kuma tankaxe shi ta hanyar shari'a, da ilimin
kimiyya sannan a amince da abinda ya dace.
4.
taimakawa jama'a ko mutum xaya a nazarin mu'ujizar
Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi.
5.
haxa qoqarin manazarta a mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a
fagen ilimi.
6.
bibiyar abinda malamai manazarta suka cimma a fagen
ilimin kimiyya, da abinda suke rubutawa ,da watsawa na
fannin mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi
7.
haxa dangantaka da masana ilimin musulumci da na kimiyya
na duniya musulmai da waxanda ba musulmai ba
8.
saduwa da qungiyoyimasana ilimomin musulumci da na
ilimin kimiyya da kuma musayar ilimi.
9.
buga littafai da majallu masu alaqa da mu'ujizar
Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi
10.
haxa taruka da kwasa kwasa na qarawa juna ilimi afagen
mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi watsa bincike
da nazarin da suka tabbata awaxansu taruka daban daban.
11.
watsa bincike da nazarin da suka tabbata ta hanyoyi da
suka dace da irin tunanin mutane da matsayinsu na ilimi
da wayewa.
12.
taimakawa masu da'awa da 'yan jaridu a duniya –jama'a ko
mutane- da nazarce nazarce don suyi amfani da ita wurin
aikinsu.
13.
taimakekeniya da qungiyoyi dabam dabam na ilimi da kuma
shirya taruka da masu nazarin mu'ujizar Alqur'ani da
Sunna a fagen ilimi
14.
qoqarin shigar da wannan nazarce nazarce cikin manhajar
makarantu da wuraren ilimi da qungiyoyi na duniya , ta
hanyar jawo hankalin waxanda abin ya shafa..
15.
Karfafa gwiwar jami’oi game da ba da dame da karfafa
gwiwa na karatu mai zurfi, da kuma gabatar da gudunmuwar
dammar bincike game da mu’ujizar ilimi a Alkur’ani da
sunna.
|