|
Jawabin
babban sakatare:

Jawabin
Dokta/ Abdullah bn Abdul Aziz Almuslih
Babban
sakatare qungiyar mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi ta Duniya.
Da sunan
Allah mai Rahama mai jin qai
'yan uwana maza da mata: maziyarta wannan shafi mai albarka…
jama'an
mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi.. a duniya baki xaya..
gaisuwa
irin ta addinin musulumci, Assalamu Alaikum Warahamatillahi Ta'ala Wa
barakatuhu..bayan haka:
manazarta mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi na duniya sunyi
gangami ayau da gabas da kudu suka taro a garin Ka'aba, qarqashin inuwar
haramin makka mai alfarma, a zaurukan kungiyar tarayyar kasashen musulmi
don a kafa wannan qungiyar mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi ta
Duniya.
Haqiqa
ilimi ne. shin akwai wanda zai qi ilimi indai ba wawa ba.
Haqiqa
sakankancewa ne(yaqini) shin akwai wanda zai qi yaqini, indai ba wanda
ya riqi jahilci aboki ba.
Haqiqa nazari ne da duba zuwa ga ayoyi biyu masu kammala juna :ayoyin
nazari da ayoyin rubuce. Ayace a duniya da dutum da rayuwa acikin
tsarinta mai ban mamaki, awannan duniya mai faxi .. mai yin tasbihi ga
Ubangijinsa.
Ayoyin Alqur'ani da Sunna ita ce zancenmu gameda haqiqa da ilimi acikin
wannan tsari da zubi na duniya, kuma zai iya ya sauka awani zamani wanda
Dan Adam ba shi da ikon da zai iya fahimtarsa ko sanin waxannan
ilimomi..
Waxannan
hujjoji ne da suke tabbatar da cewa wanda ya halicci wannan duniya
haqiqa shine wanda ya saukar da Alqur'ani.
Sakon wannan shafi na duniya shine ya bayyana wannan haqiqani mai
haske, koda yaya ya kasance don kara cigaban ilimi da kuma tabbatar da
amfanin mutane afagen nazari don amfaninsu duniya mu kuma tabbatarwa da
duniya cewa addinin mu addinin ilimi ne da nazari, kuma yana neman
gaskiya ne yana kuma kira zuwa ga cigaban da qirqira da kuma riqo da
dalilai, da kuma cigaban halara don gina rayuwar mutum mai alafarma da
karamci,qarqashin adalci kuma ilimi yayi wa alumma hidima, ba masu
ruguzawa ba ne, saboda haka mutane duka zau zama cikin aminci da tsaro."
Lalle wannan Alqur'ani na shiryatarwa zuwa ga mafi daidaituwa,kuma yana
yiwa muminai bishara waxcanda suke nagari cewa suna da lada mai girma".
Amma
ku jama'a malamai manazarta da kuma jama'ar wannan shafi…
Ya ku
waxanda suke da alaka da wannan shafi to naku ne kuma daga gareku yake
dominku ne, kuma gaisuwa ta da sauran 'yanuwa da sauran manazarta da
malamai daga qungiyar mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi ta
Duniya., kuma muna baku dukkan girmamawa saboda kune shaidun Allah da
rububiyarsa da uluhiyyarsa da sunayensa da siffofinsa da ni'imominsa(
Allah ya shaida cewa babu sarki sai shi haka mala'iku da ma'abuta ilimi
suna tsaye da adalci, babu sarki sai shi mabuwayi mai hikima).
Wannan kungiya ta haxa gaggan malamai da manazarta masu matsayi afagen
ilimi mu'ujizar Alqur'ani da Sunna, awannan fage akwai manyan masana
waxanda suke da zurfin ilimi a cikin addininmu na ma'aiki (s.a.w) don
kuma su kira duk wani wanda yake da iko ko baiwa ta bin wannan turba
madaidaiciya da kuma bayyana gaskiya da fitar da ita da kuma fitar
haqiqar da Allah(s.w) ya sanya a duniya cikin halittunsa na abinda zai
amfani mutane ya kuma qarawa masu imani imani(shine wanda ya halicci
maku abinda ke cikin qasa duka),(ka ce ku dubi abinda ke cikin sammai da
qasa).
Haqiqa wannan qungiyar mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a fagen ilimi ta
Duniya ta na bin manhaja na ilimi da nazarin mu'ujizar Alqur'ani da
Sunna a fagen ilimi, zamu taqaicesu kamar haka:
1-sun
qetare fagen hasashe da kirdade sun isa zuwa ga haqiqa wacce ba ta
karvar shakku.
2-kuma an
sami dalilai abayyane acikin Alqur'ni dea Sunnar manzo(s.a.w)
3- haxa
tsakanin wannan kaqiqar da ma'anar nassi ta salo mai sauqi.
4 kuma
wannan ma'ana ya dace da harshen larabawa, wanda Alqur'ani ya sauka da
ita.
5- ba ma
binciken abubuwa na gaibu wanda Allah ne ya kevantu da sanin waxannan
abubuwa, kuma mu muka yi imani dasu.
6- fassara
Alqur'ani da Alqur'ani sannan da Sunna ingantacciya sannan bayanan da
suka inganta daga magabata na Alumma sannan ma'anar larabci da Alqur'ani
ya sauka da ita.
Muna so muyi qarin bayani anan game da kokwanto da aka tada gameda
fassarar kimiya- da kuma abinda ya gabata na mu'ujizar Alqur'ani da
Sunna- duka suna bayani ne akan irin nazarin da ba a tantancesu ba da
yadda manazarta suka yi gaggawa wurin faxin wasu ra'ayoyin ba tare da
sun taka tsantsan ba, duk da cewa irin waxannan abubuwa da suka auku
kaxan ne basu da yawa, saboda haka qungiyar mu'ujizar Alqur'ani da Sunna
a fagen ilimi ta Duniya duk lokacin da zata duba wani nazari takan sanya
shi awurin da ya dace ta kuma faxi sharuddansu .
Lalle
wahalar da ake fuskanta gameda wannan bincike har akai ga samar da
waxannan bayanai na ilimi,duk ba wani abu bane alokacin da zamu ga
amfanin abin yana bayyana afilin game da mu'ujizar Alqur'ani da Sunna a
fagen ilimi, ya zama dole muyi nuni da wasu daga cikin su ko manazarta
zasu qasa himma don gano haqiqa:
1-tasirin
da wannan abu ya bari azukatan musulmi, da kuma qaruwar yaqininsu
alokacin da suke ganin waxannan ayoyi da dalilai abayyane da suka zo
daga harshen manzo(s.a.w), wannan yana qarfafa gwiwa wurin riqo da
Alqur'ani da sunnan masu tsarki do bin shiriyarsu.
2-maida
martani na ilimi mai qarfi ga masu shakka acikin gaskiyar saqon
musulumcin muhammadiyya, saboda bayyana irin waxan nan bayanai na ilimi
wanda manzo(s.a.w) ya bada labarinsu shekaru dubu da xori da suka gabata
a lokacin da babu wani cigaban ilimin zamani da za a iya gano waxannan
bayanai,to wannan kawai ya iso ya gamsar da masu adalci na malamai su
san cewa Alqur'ani daga Allah yak, kuma da gasgata manzo (s.a.w)
3-raddi da
kwararan dalilai da za su yi nuni da cewa addinin musulumci dinin ilimi
ne – duk kuma da kiran da manzo yayi ga falalar ilimi da malamai-to ya
faxi wasu kuma bayanai na ilimi na duniya da na halittu, babu kuma wanda
ya iya gogesu afagage da dama acikin hadisai masu inganci akayi waxannan
bayanai da ayoyi.
4-mu'ujizar fagen ilimi itace hanya mafi sauqi wurin qara himman
musulmai don su cigaba da bincike na cigaban ilimi don a qara samun
faxaxa fahimtar ayoyi da Hadisai.
5-kamar
kuma yadda wannan fage zai zama babban qofa ta da'awa wanda zai buxe
sauran qofofin na da'awa a wannan zamani da muke ciki na ilimi, wanda ke
sanya jama'a da dama shiga musulumci daga yahudawa da nasara – kuma da
damansu sun fara sanin musulumci ne ta hanyar wannan ilimi.
6- babu
shakka komawa zuwa ga addinin musulumci ga waxanda suka rafkana ko suka
gafala , ko kuma musulumtar waxanda ba musulmi ba , duka ya faru ne
lokacin da musulmai suka koma ga addininsu suka yi riqo izza da karama
acikin al'umma bayan wani rotse da suka samu bayan halifancin musulumci
, da mamayar mulkin mallaka.
7-wannan
duka na tunasar damu hadisin manzo (s.a.w) da yake cewa (wasu daga cikin
al'ummata ba za su gushe ba suna yaqi akan gaskiya, suna fuskantar wanda
yayi fito na fito dasu. Har sai sun yaqi na qarshensu Masihul dajal,
kuma ba ruwansu da wanda ya sava masu ko ya tozartar dasu har sai
al'amarin Allah ya zo) .
mu
awannan shafio na duniya muna gabatar da da'awa ce ta duniya ga gaggan
malamai da manazarta da masu bada mahimmanci ga mu'ujizar Alqur'ani da
Sunna a fagen ilimi. Kuma muna so su taimaka mana da iliminsu da
shawarwarinsu da nasihohinsu, muna fata duka za muyi ta rayya da ku
awannan fage, haka kuma muna kira ga yanuwa da suke zaune a qasashen
waje waxanda ba na musulmi ba su zamo masu kira na gari da hanyar amfani
da wannan hanyar ta da'awa, su kuma fa'idantu da wannan shafi da nazarin
da aka gabatar aciki, muna fata zamu bada gudunmuwa don bunqasa wannan
shafi don cigaba amin.
Wannan
kira ce daga wannan shafi ta duniya muna fata zamu sami karvuwa acikin
shafuka ta duniya wasu aiki da Alqur'ani da sunna mai tsaki.
Ya 'yanuwa
maza da mata ku zamo mataimaka wannan lamari .
Allah yasa
mu dace.
|