|
Fuskacin mu'ujizar:
Kamar yadda aka sani cewa mututane a irin lokuta da suka
gabata alokacin wahayi ba su san abin da yake faruwa wa
na yanayi samaniya da iskar gaz da ya ke yaxuwa,
balle har su san cewa idan aka yi bisa yana raguwa, ko
qasa yana
qaruwa
ba. Balle har su san cewa okusijin na da mahimmanci ga
rayuwa ba duk lokacin da aka yi bisa buqatuwa
gare shi yana
qara
qaruwa.har idan
aka ce mutum ya rasa shi zai kai shi ga rasa iya
nunfashi abinda zai kai shi ga hallaka.
Kai
mutane ma sun kasance suna zaton cewa duk lokacin da
mutum yayi bisa ya fi kusa da iska, kuma
qirjinsa zai fi
walwala.
Ayar Alqur'ani
kai tsaye na mana nuni ga wasu haqiqa
biyu, waxanda
Ilimin zamani ya tabbatar dasu:
Na
farko:
quncin
qirji da wahalar
nunfashi,a duk lokacin da mutum yayi sama a sararin
samaniya, daga baya aka gano cewa saboda raguwar
okosajin ne.
Na
biyu:irin turnuqewa
dake rigayar mutuwa lokacin da mutum ya sami kansa a
bisan samaniya na nisa
qafa dubu talatin,
saboda matsanancin buqatuwar
okosojin masu shiga huhu, daga nan mutum zai kai ga
hallaka.
Gami da
qari
kalmar da Allah yayi amfani da ita wato"hauhawa" abin da
ke
qarawa abin
qarfi
da tsanani, don ya bayyana yadda yanayin wahalar da mai
hawa sama yake fuskanta . shin wannan haqiqa in banda
Allah (s.w) wa zai iya sanar damu ita. Lalle wahayi ne
daga Allah. |