|
Fuskacin mu'ujiza:
Da
can mutane suna da wani camfi da suke yiwa koguna da
teku , kuma masana ruwa na wancan likacin basu da
cikakken masani game da abin da ya shafi yanayin ruwa da
sassayawarsa, mai zurfin gaske.
abinda yasa wasu suke yin camfi a irin waxannan
ruwa marasa tafiya sukan ce akwai waxansu
kifaye ne da muke riqe
jirage a irin wannan wurare, kamar yadda romawa na da
sukan ce.duk da cewa suna sane da cewa kaxawar
iska na tasiri acikin harkokin taguwar ruwa, amma duk da
haka zai masu wahalar fahimtar teku mai zurfin gaske,
kamar yadda nazari ya tabbatar da cewa ba afara bincike
mai zurfi gameda ruwa ba sai atsakiyar
qarni na ashirin,
yayinda aka gano irin zurfin ruwa da duhun da yake ciki
da abubuwan da suke faruwa sakamakon duhun.amma wannan
aya ta Alqur'ani
mai girma tayi nuni ga waxannan
abubuwa biyu.
Haqiqa
ayar tayi nuni ga zurfin teku da duhunsa da kalmar"teku
mai zurfi" masu tafsiri suka ce: abinda ake nufi da waxannan
duffai sune: duhun girgije, da duhun taguwar ruwa, da
duhun teku. Duk wanda ya kasance a
xayan wuraran nan
uku ba zai ga komai ba" amma giragizai masu yawa da suka
kare wannan teku, ita kuma taguwar ruwa tana rufe sauran
hasken ta haka duhun ya ke faruwa hatta kifaye da suke
wannan yanayi Allah ya haliccesu da wani jiki mai
haskaka masu hanyarsu:" duk wanda Allah bai sanya masa
haske ba ba zai tava
samun haske ba"
Kuma Allah ya yi nuni ga yanayin motsin tekun da faxinsa"
acikin teku mai zurfi, wanda taguwar ruwa ta rufe shi,
abisansa akwai wata taguwar" ma'ana taguwar tana rufe
tekun mai zurfi wannan shine haqiqanin
abinda masana na zamani suka gano na cewa ruwa mara
zurfi yayi dabam da ruwa mai zurfi ,abinda ba a gano ba
sai nan da shekaru
xari da suka
gabata kawai.
amma waxannan
bayanai duka Alqur'ani
yayi nuni garesu filla filla a
qarni goma sha huxu
da suka gabata. To wanene ya baiwa muhammad (s.a.w)
wannan labari ? shine Allah (s.w). |