|
Haqiqar
ilimi:
Taurari idan suka riqa
suna kai wani munzali da suke tsufa ana kiransu da
(Black Holes) sukan sami huji baqi
wanda yake da girman gaske wanda yafi girman rana da
ninki biyar,kuma tana da
qarfin maganaxisu
awannan lokaci ta inda take janye duk wani abu da yayi
kusa da ita da kusan kilomita(dubu 300 acikin daqiqa)
shi yasa ake kiranta da ramuka masu janye dukkan wani
abu da yayi kusa dasu, na kananan taurari(Giant
vacum-Cleaners)
wato suna share duk wani abu da yayi kusa dasu kamar
yadda(Karl Schwars ) a shekara1916 da kuma(Child)
ashekara ta 1934, a kuma shekata ta 1971(Oppenheimer
Robert) ilimi ya tabbatar da cewa idan tauararuwa ta
soma tsufa takan yi huji baqi
inda take haxiye
duk abinda da yayi kusa da ita. |
|
Fuskacin mu'ujiza:
Salon Alqur'ani
mai girma na kore rantsuwa, kamar yana cewa ne ba sai
na rantse da abinda kowa yake ganini
qiriqiri ba,
wannan salo kuma ya
qara tabbatar da
cewa Alqur'ani
wahayi ne na Allah da yake cewa" ba sai na rantse da
taurari masu tafiya ba* masu gudu suna
vuya* da dare
yayin da yayi duhu da safiya yayinda tayi haske* lalle
shi maganan manzo ne mai girma"(at-takwir 15-19) kuma
duk abinda Allah ya rantse dashi to lalle abin nada
mahimmanci wurin kafa hujja dashi, annan wurin abin da
aka faxa
ya dace da hujin taurari ko tsufarsu kamar yadda ake faxi,shi
yasa sifata su da aka yi da (masu gudu) ya dace da gudun
da suke yi,amma kalmar(masu
vuya) ita ma ta
dace da abin da yake faruwa mata na
vuya da
vacewa
da tsufa ko mutuwa bayan ta girma ta zama abar
sha'awa.kuma haka abin yake kasancewa lokacinda
tauraruwa ta shufa sai ta sami wani hujji ta kuma
vace baki
xaya
ta zamo bata da haske, saboda tana janye dukkan wani
haske da yabi kusa da ita. Shi yasa aka kira su da sunan
"masu gudu suna
vuya" anan zamu ga
Alqur'ani
ya sifatasu da siffofi da suka dace abinda ilimin
taurari na zaamani ya gano, abinda yake tabbatar da cewa
wannan magana ne na Allah (s.w). |