|
Haqiqar
Ilimi:
Yizga a cikin ilimin halittu ( shi
ne faifan farko):
Ilimi halittu ya tattabar da cewa
yizga shi ne faifan farko acikinsa ne ake haxa
jariri lokacin da zai zama tayi sannan har a sami
qashin
bayansa bayan da shi wannan faifan ya
vace .
Haxa
faifan farko: A rana ta goma sha huxu
igiyoyin ciki da na waje na tayi za su fara haxewa
su zama kaman yana yi gwaiba a dunqule
sai qasan
ya yi faxi
kasan kuma ya tsuke sai
qasan
ya zama ya yi wutsiya kaman na gwadari ta nan wannan
faifan farkon yake haxuwa
a rana ta goma sha biyar.
Daga nan kuma sai ya fara
rarrabewa ya fara toho jijiyoyi su yi yawa dama da hauni
bayan haka ya faru ne sai asami
qashin
baya kuma a fara samun tsiran gavovin
jariri. Amma idan ba a sami haxuwar
wannan faifan ba za a sami tuhuwar gavovin
jariri ba, balle har a sami wani
qashin
baya.
Saboda mahimmancin wannan faifan
kwamitin ilimin halittan tayi na Ingila suka sanya
lokacin da likitoci zasu iya samin lokacin da zasu iya
bincike da gwaje gwaje game da jariran da ake rainonso a
kwalba. A lokacin da wannan faifai ya fito saboda kai
komo da motsin da zai riqa
yi za aga bayyanar abubuwa kamar haka:
A lokacin da za a rufe wannan
kwalba za a ga bullan faifan kunne da alamun ido.
Kwakwalwa kuma na haxuwa
asaman wannan bututun jijiyar sai ya samar da
vargo
a yankin qasa
sai afara samun ginuwar
qashi
kwakwalwa.
Wato dai ataiqaice
wannan faifan farko
xin
shi ne babbabr alamar fara halittan jariri kuma daga
baya zai fara dishewa har ya zamana ba a ganinsa da ido
sai dai da madubi likita a lokacin da aka sami ginuwar
kashin baya kenan . |