|
Haqiqar
ilimi:
Binciken ilimi da aka yi da dama
sun tabbatar da cewa: a lokacin da wani abu ya sami
jiki na haxari
ko jin ciwo akwai wasu hanyoyi da sauran gavuvva
suke ba da gudumuwar kariya ga wannan gavar
da ta kamu.
Kuma wannan kariya da gudunmawa ya
danganta ne gwargwadon girman ko
qanqancin
ciwon, duk lokacin da jin ciwon yayi
qarfi
a lokacin bada gudunmawar ke
qara
karfi haka kuma idan abin ya zamanto
qarami
ne haka lamarin yakan kasance.
Misalin lokacin da aka sami wani
rauni agava
sai kwakwalwa ta kira wasu
vargo
dake ciki su su zuba wasu abubuwa waxanda
za su kare wannan wurin rauni daga shigan wani irin
kwayar cuta, da kuma wasu abubuwa mai danqo
da zai riqa
zuba don ya sanya wurin yayi saurin warkewa ataqaice
ko yane vangaren
jiki zai riqa
bada nasa gudunmuwa na abin da yake dashi don wannan gavan
da yake da rauni ya sami sauqin
warkewa ta hanyar gudunmawa da taimakekeniyar sauran gavovin
nasa. Wannan shi ne abin da haqiqanin
ilimi ya tabbatar da shi a likitance. |