|
Fuskacin mu'ujiza:
Mutane a zamanin ma'aiki (s.a.w)
da kafin zamaninsa sun kasance suna kudurta cewa- har
lokacin da (baster) ya gano makrobat- wannan cuta
aljannu ne iskoki ko taurari suke kawo ta ba ta da wani
alaka da tsafta ko kazanta ko wani yanayi, saboda haka
ba sa yarda da cewa kwayoyin cutan zasu iya tashi daga
mutun zuwa wani,sai suna neman mata magani ta hanyar
tsibbu da bori tsafi.
awannan yanayin ne ma'aiki
(s.a.w) ya kawo wata ka'ida wacce ta zama asasin ilimin
riga kafin kariya na zamani, bayan da aka gano dalilan
da suke sanya cutukan da annobar, wato riga kafin
kariya, don hana watsuwar annoba a wasu biranen ko
gungun wasu mutanen. Ma;aiki (s.a.w) shi ya tabbatar da
wannan hakikanin ilimin acikin hadisinsa" (idan kuka ji
annoba awani gari kada ku shige shi,idean ya auku a wani
gari kuna cikinsa kada ku fita daga ciki) Buhari da
Muslim suka ruwaito.
Don a kara tabbatar da wannan
wasiyar ta Ma'aiki (s.a.w) ya gina kango mai karfi a
wurin annoba yayi wa wanda yayi hakuri ya zauna awurin
annoban da ladan shahidai, kuma yayi wa wanda ya gudu
daga wurin alkawarin narkon azaba da cewa: "mai gudun
annoba kaman mai gudu ne daga yaki, wanda yayi hakuri
yana da ladan shahidi."Ahmad ya ruwaito.
Idan akacewa mutum lafiyayye a
shekaru xari
biyu da suka gabata, alhalin yana ganin masu ciwo na
mutuwa a gefensa, kuma yana cikin
qoshin
lafiyarsa ace masa: ka zauna kada kabar inda kake . da
sai yace wannan maganan hauka ne ko kuma ba a
qaunarsa
da rayuwa, zai zabura ya gudu zuwa wurinda babu wannan
annoba , saboda haka mu musulmi ne kawai muke zama
alaokacin da annoba ya faru muna aiwatar da maganan
manzonmu (s.a.w). har sai lokacin da ilimi ya gano haka
aka fara amfani da wannan sabon ilimin da aka gano
alokacin da mu musulmi mun jima muna aiki da wannan
koyarwar manzo(s.a.w)
Shin akwai wanda zai iya bada
wannan bayani aqarni
goma sha huxu
da suka gabata ? in dai ba wanda yake da wahayi na
ubangiji ba!! Allah (s.w) na cewa " ka ce godiya ta
tabbata ga Allah, zai nuna maku ayoyinsa kuma zaku sansu
, Ubangijinku ba mai rafkana ba ne ga abinda kuke
aikatawa)(an-namli 93). |