|
Haqiqar
ilimi:
Harvey
shine farkon wanda ya fara nazari akan
xan
tsakon kaza ta hanyar amfani da gilashin a shekara ta
1651, sannan kuma ya yi nazari akan tayin barewa
saboda wahalar da ya fuskanta wurin sanin haqiqanin
yadda ciki yake a farkon kamuwarsa, sai ya tabbatar
dacewa ciki wani yanayi ne na kumburin mahaifa. ashekara
ta 1672 wani malami wai shi Graaf ya gano
qwayaye
a mahaifa waxanda
ake kira da" Graafian Follieles", kamar yadda ya gano
wasu kafafe acikin mahaifar zomo masu ciki, daga nan ya
gano cewa ciki ba kumburin mahaifa bane . aa kwayayene
da suke kyankyasuwa acikin mahaifa wato Blastoeysts. A
shekara ta 1675 wani malami mai suna Malpighi ya gano
ttayin tsako acikin kwan kaza amma yaga cewa baya buqatan
maxadin
kyankyasa daga namiji.ya gano cewa yana kara girma amma
ba akan matakai ba. Ta hanyar amfani da madubin likita
Leeuwenhock ya gano yadda kwayayen mutum ke ginuwa a
matakin farko ashekara ta 1677,amma ba su gano yadda
abin ke kaiwa har likacin haihuwa ba.,amma dai sun gano
cewa tayi na hauhawa daga mataki zuwa mataki. A shekara
ta 1759 Wolff yayi hasashen yadda jariri ke girma akan
matakai .
ashekara ta1775 aka
qarasa
rikicin cewa jariri ba lokaci guda yake haxuwa
ba sa ya bi wasu matakai bayan gwajin da Spallanzani
yayi akan wasu kwayoyin halittu . a shekara ta 1827
bayan shekaru 150 kenan aka gano cewa wani malami
Von
Baer ya gano kwayaye acikin wata karya mai ciki . sannan
a shekara ta 1839 Schleiden da Schwann suka gano yadda
hallittan bil adam ke hauhawa mai suna CELLS. Daga baya
aka gano yadda haqiqanin
lamarin yaketa hanyar haxuwar
kwayayen mace da maniyin namiji,. |