|
Fuskacin mu'ujizar:
Nassoshin
qur'ani
sun tabbatar tun shekaru dubu da
xari
huxu
da cewa akwai bambanci tsakanin tauraro da kaukabi
kamar rana da wata, kuma shi ne abin malaman falaki suka
tabbatar a wannan zamani namu bayan da aka samu wasu
abubuwa na gwaje gwaje da hange hange da abubuwan
xaukan
hoto na haske a cikin
qarnoni
kadan da suka gabata. Tauraro dai jiki ne mai haske a
sama wanda yake fidda haskensa daga cikinsa, amma
kaukabi shi fidda hasken da yake amsa daga rana da
taurari ya ke yi,kuma wannan abin haka ma sauran
kaukabai suke yi.
Rana kamar wani babban makamashin
nokiliya wanda yake yawa a sararin samaniya cikin saurin
gaske tana da haske da zafi mabambanta a yawanu da
yanayinsu, ba wani jiki ne mai matabbacin haske ba . a a
shi jiki ne mai haske mai yawan juyawa( mun sanya fitila
mai juyawa) Al- Nabai 13.
Amma wata jiki ne wai fitar da
hasken rana sai ya haskaka duhun duniya. Wannan shi ne
abin da Alqurani
ya tabbatar a cikin waxannan
ayoyin biyu. To wanene ya sanar da Muhammad (S.A.W) waxannan
bayanan na ilimi? Haqiqa
sai dai Allah sarki mabuwayi. |