|
Imam Muslim ya ruwaito daga
Abdullahi bn Farukh , cewa ya ji Aishat na cewa
:Manzo(s.a.w) ya ce: an halicci dukkan Dan adam akan gavuvva
xari
uku da sittin.wanda yayi kabbara yayi hamdala yayi
salati yayi tasbihi, ya kuma nemi gafarar Allah. Ya cire
dutse akan hanyar mutane ko
qaya
ko qashi
daga hanyar jama'a, yayi umurni da alheri yayi hani ga
abin qi,bisa
waxannan
gavovi
xari
uku da sittin, to zai tafi rananr an nisantar dashi
daga wuta.
Imam Ahmad ya ruwaito a mu7snadinsa daga Abdullahi bn
Yazid yace: na ji Abu yazid na cewa naji Manzo(s.a.w)
yana cewa:" mutum nada gava
xari uku da
sittin, saboda haka ya wajaba yayi wa kowa ce gava
sadaka". Sai suka ce wanene zai iya haka ya Manzon
Allah? Sai yace: ka fizne kaki a masallaci, ko ka kauda
wani abu akan hanya, in kuma baka iya ba Sallar wahala
ta isheka" (musnad Ahmad 23700). |
|
Fuskacin mu'ujiza:
Manzo (s.a.w) ya bada labarin
yawan gavuvva
da suke jikin mutum
xari
uku da sittin,alokacin da yake babu wani mahaluqin
da zai iya sanin haka , tunda gavovi
suna da gqananan
wurare da yake da wuyan sanin yawansa sai dai idan anyi
aiki da wasu kayayyakin bincike, ba wai kawai da idanu
ba, kamar yadda masana ilimin fixa
suka tabbatar, ma'anar gava
kamar yadda malam harshe suka tabbatar shine: mahaxa
qasusuwa
,kuma Manzo (s.A.W) ya bayyana haka acikin
qarni
goma sha huxu
da suka gabata .wannan yana daga cikin ayoyin wahayi da
mu'ujizar manzo (s.a.w). |