|
Fuskacin mu'ujizar:
al'adu suna da munanan
xabi'u kuma ana
kyamarsu hatta ma ga masu bautan gumaka, inda suke
sifatasu da cewa suna kashe Allolin alheri, tatsuniyoyi
na cewa Alade ne ya kashen Horus na misirawan da, da
Adwan na Kan'anawa . da Odonis na Girkawa, da Itis na
mutanen Asiya . kuma misarawan da suna kallon masu kiwon
Aladu mutanene mara
qima da
kamala,hakan nan kuma masu kiwon Aladu ba sa auren kowa
sai yasu-yasu, kuma dukkan wanda ya shafi Alade yayi
wanka.
Haka ma an harantawa Ahlul kitabi cin Alade duk da cewa
sun savawa
addinin. Amma addinin musulumci ya bayyana dalilin
haranta naman Aladeda cewa (qazanta ne)ko
cuta ko najasa duk ta kumshi wannan ma'ana ayoyi har uku
suka bayyana haramcin naman Alade: Allah (s.w) na
cewa"lalle an haramta maku mushe da jini da naman Alade
, da abin da aka yanka don wanin Allah, wanda ya ya
matsu ba mai
qetare iyaka ba ko
shisshigi to lalle Ubangijinka mai gafara ne mai jin
qai" (An-nahal
:115) .
Allah (s.w) na cewa "an haramta maku mushe da jini da
naman Alade da abinda aka yanka don wanin
Allah…"(Al-maida 3).
Kuma haramcin ya kunshi kitsensa da aka haramtawa
yahudawa kawai ya nuna mana cewa ya shafi namansa kamar
yadda Allah (s.w) yake cewa: " ga yahudawa mun haramta
duk wani abu mai akaifa,daga shanu kuma da awaki mun
haramta masu kitsensu ko abin baynasu ke
xauke dashi ko
kayan ciki ko abinda ya cakuxu
da
qashi, wannan
mun sakanya masu da shisshinsu lalle mu masu gaskiya ne"
(Al-an'am 146).
Haranta kitse ya
qumshi haranta
nama koda ko kamar raugar dabbobi ne da mutum zai ci .
alokacin da Al'qur'ani ya
sauka mutane ba su san haxarin
da Alade ke
xauke
dashi ba, ta yaya zamu sami wannan garkuwa in dai ba ta
hanyar ilimin da Allah maxaukakin
sarki ya saukar mana da shi ba.:" Al'ummanka suka
qaryata dashi kuma
shi gaskiya ne.ka ce ni ba madogaranku bane, kuma ko
wane labari na da matabbaci da sannan ya ku sani" (
Al-an'am 66). |