|
Haqiqar
ilimi:
An
yi amfani da Habbat Sauda'a - a kashen gabas ta tsakiya
da ta nesa- a matsayin magani, tun da shekaru dubu biyu,
kuma aka tatso sinadarin Nijillun daga man Habbat Sada'a
a shekara ta 1959 ta hannun Aldakhakhaniy da abokansa.
A
cikin kwayan Habbat Sauda'a akwai daskararren mai da ya
kai nauyi 40% da 1,4% mai narkakke, kuma yana dauke da
sinadarai goma sha biyar:aminiya, protein, calsium,
karfe, sodium, da portasium ,kuma mafi mahimmancin
sinadarinta shine:- siymokiniyon,daysiymkinon,saimo
haidrokiyon da saimol.
Ba
a fara sanin amfanin Habbat Sauda'a ba wurin karfin
garkuwan jiki ba sai daga shekara 1986 bayan da Dakta Alqady
da abokansa a Amirka. Sannan aka ci gaba da yin
bincike daga baya a kasashen duniya da dama,a fagage
daban daban game da wannan tsiron, Dakta Alqady
ya tabbatar da cewa Habbat Sauda'a yana tasiri wurin
qarfafa
tasirin garkuwar jiki, an gano cewa yana kara
qaimi
jijiyoyi kusan 72% kuma ya
qara nashaxin
wasu garkuwoyi masu yaqi
da cuta,kusan 74% kusan dukkan binciken da aka yi daga
baya sun
qarfafa bayanan da
Alqady
daga ciki:
Abin da wata jaridar garkuwan jiki ta duniya ta rubuta a
bugun Agusta 1995 game da tasirin habbat sauda'a a
jijiyoyi masu
qara
qaimin mutum
daga cutuka da dama , da kuma kara
qaimin
jijiyoyin jini daban dabam. Da kuma abin da majallar ta
buga a bugunta na satumba 2000 game da bincike goma na
tasirin man habbat sauda'a ga garkuwar cutar eytomegalovirus.
A lokacin da aka zavi
man habbat sauda'a don maganin wannan cutar , aka gwada
bangaren da ya kamu da cutar afarkon kamuwarsa, ta
hanyar tantance jijiyoyi masu kashe cutar aka auna
tasirin man habbat sauda'a game da shi.ita ma majallar
kansa ta turai a bugunta ta Octoba 1999 ta buga wannan
bayani ta hanyar gwajin kansar ciki ta
veraye.
Haka ita kuma mujallar binciken maganin kansa a bugunta
na mayu 1998 ta bayyana cewa man habbat sauda'a yana
maganin kumburi da kansa. Haka kuma majallar magani ta
Isno ta buga a adadinta na Afrilu 2000 game da tasirin
man Habbat Sauda'a da kwayarsa game da maganin cutuka
da dama. Haka ita ma majallar tsirrai na magani ta
fabrairu 1995 ta yi bayani game da binciken ta ya
tabbatar ta anfanin Habbat Sauda'a game da taimakawa
gudun jini da tacewarsa da sauran bincike da dama da aka
gudanar. |
|
Fuskacin mu'ujiza:
Manzo (s.a.w) ya bamu labarin cewa: Habbat Sauda'a
maganin dukan cutuka ne kuma kalmar maganin sai ta zo a
sigar nakira a dukkan hadisan da suka zo, kuma ya zo a
sigar tabbatarwa ba korewa ba saboda haka zamu fahimci
cewa habbat sauda'a magani ne na kowa ne yanki na cuta ,
kuma ilimi ya tabbatar da cewa garkuwar jiki shine yanki
da yake kare mutum daga mafi yawancin cutuka, wato
garkuwa na asali koko wanda aka
qarfafa shi da
wasu abubuwa, wanda zai
qara masa
qarfi
na yaqi
da abubuwan da suke kawo ciwo.
Kamar kuma yadda ya tabbata a bincike na ilimi da aka
gudanar cewa Habbat sauda'a yana
qara
qaimin garkuwar
jiki kuma yana
qarfafa jijiyoyin
garkuwa kusa kashi 75% a binciken da Alqady
yayi.kuma sauran bincike daga baya ya
qara tabbatar da
haka, ta hanyar gwajegwaje da akayi ya magance tsutsan
ciki da kansa da tsargiya da macijin ciki da sauransu ,
da kuma
qara gudun jini ta
hanyar kyautatashi, da kara
qarfin jijiyoyi
abin da zai tabbatar da cewa maganine na dukkan komai.
Ta
haka zamu ga haqiqanin ilimi
ya bayyana a cikin wannan hadisin abin da yake ba wani
wanda zai iya gane haka balle har ya faxa
ya kuma sanar da mutane tun
qarni goma sha huxu
da suka gabata indai banda Manzo (s.a.w) wanda yake
manzo ne daga Allah . kuma Allah ya yi gaskiya da ya
kira shi da cewa ( Kuma ba ya yin Magana daga son
zuciyarsa.* (Maganarsa) ba ta zamo ba, face wahayi ne
da ake aikawa.*) (Al-Najm 3-4) |