Kungiyar mu’ujizar ilimi na Alqur’ani da Sunna da duniya    
Saqonmu: Fayyace mu’ujizar ilimi na Alqur’ani da Sunna ta duniyia da bayyana shi game da dukkan mutane

Language

 
Nazarin a takaice game da kungiyar Tuntubemu  

 
   

       Jawabin babban sakatare

 

Allah (s.w) na cewa : Yusuf ya kai mai gaskiya bamu fatawar shanu bakwai mai qiba suna cin bakwai busassu, da zangeru bakwai koraye da wasu busassu , ko zan koma ga mutane ko zasu sani* yace zaku yi noma shekaru bakwai a jere duk abin da kuka girba ku bar shi acikin zungeransa sai kaxan daga wanda zaku ci* Sannan wasu shekaru bakwai na fari zasu zo, sun cinye abin da kuka gabatar masu sai kaxan daga cikin waxanda kuka killace* sannan wani shekara zai zo mutane za su nemi gudunmuwa aciki zasu yi lallage)

Allah ta'ala yana cewa: me yasa ba ku neman daraja daga Allah * lalle ya hallice ku a matakai(nuh 13-14).

Allah (s.w) na cewa: wanda Allah ke son ya shiryar dashi sai buxe zuciyarsa da musulumci, wanda kuma yake so ya vatar dashi zai sanya qunci a qirjinsa kamar mai hauhawa zuwa sama, haka Allah ke sanya datti akan waxanda ba sa yin imani" (al-an'am 125)

Allah (s.w) na cewa :lalle waxanda suka kafirce da ayoyinmu da sannu zamu qona su da wuta, a duk lokacin da fatar su ta nuna sai mu sauya masu fata sabuwa , don su xanxani azaba, lalle Allah ya kasance mabuwayi ne mai hikima (an- nisa'I 56)

Imam Muslim ya ruwaito daga Abdullahi bn Farukh , cewa ya ji Aishat na cewa :Manzo(s.a.w) ya ce: an halicci dukkan Dan adam akan gavuvva xari uku da sittin.wanda yayi kabbara yayi hamdala yayi salati yayi tasbihi, ya kuma nemi gafarar Allah. Ya cire dutse akan hanyar mutane ko qaya ko qashi daga hanyar jama'a, yayi umurni da alheri yayi hani ga abin qi,bisa waxannan gavovi xari uku da sittin, to zai tafi rananr an nisantar dashi daga wuta.

Allah(s.w): kace ba sami wani abu daga cikin abinda aka yi min wahayi da shi ba haramtacce, na abinci sai dai in ya kasance mushe ne ko jini n yanka ko naman alade, to shi najasa ne ko fasikanci aka yanka ba don wanin Allah. .wanda ya ya matsu ba mai qetare iyaka ba ko shisshigi to lalle Ubangijinka mai gafara ne mai rahama (Al-an'am 145).

An ruwaito daga Abu huraira cewa Manzon Allah (s.a.w) ya ce: dukkan xan Adam turvaya na cinsa sai dai kawai yizgar farko daga shi ne aka halicce shi a cikinsa ake harhaxa shi"

Allah(s.w) na cewa : na rantse da sama ma'abuciyar maidowa(al- tariq 11)

Allah(S.W) yana cewa:" da qasa ma'abuciyar tsaguwa"(altariq 12)

Manzo(s.a.w) ya ce: alfasha ba za ta tava watsuwa acikin wasu jama'a ba abayyane face sai annoba da cutuka waxanda ba tava watsuwa agabaninsu ba, sun watsu acikinsu wa ". ya kuma qara cewa "zina bai tava watsuwa acikin wasu al'umma ba face mutuwa yayi yawa acikinsu' malil ya ruwaito acikin muwaxxa.

Daga Manzo (s.a.w) ya ce: "Babu wani cuta sai yana da magani daga Habbat Sauda'a sai dai mutuwa"

Allah yana cewa:"ya garwaya teku biyu(ruwan daxi da na zartsi) suna haxuwa.* A tsakaninsu akwai shamaki, ba za su qetare haddi ba.* To, saboda wane daga ni'imomin Ubangijinku , kuke qaryatawa.lu ulu u da murjani na fita daga gare su."(19-22 Al Rahman ).

Allah ta;ala yana cewa: shi ne wanda ya tafiyar da qoramai biyu wannan mai daxi qorama, wannan kuma mao zartsi mara daxi ya kuma sanya shamaki mai shingewa tsakaninsu " Al- furqan 53)

Allah (s.w) na cewa: ko kamar dufai acikin teku mai zurfi, wanda taguwar ruwa ta rufe shi, abisansa akwai wata taguwar,abisansa kuma akwai girgije, duffai sashinta akan sashi, har in ya fitar da hannunsa ba ya iya ganinsa , duk wanda Allah bai sanya masa haske ba ba zai tava samun haske ba." (An-nur 40).

Allah (s.w) yana cewa : a'a ha idan bai bari ba zamu damqeshi a gaban gwagwalwa* kwakwalwa mai Qarya mia kuskure" Al-alaq 15-16

Allah(s.w) na cewa: ba sai na rantse da taurari masu tafiya ba* masu gudu suna vuya (at-takwir 15-16).

Allah (s.w) yana cewa: An rinjayi Rum* a mafi kusan qasa, kuma su bayan rinjayar ta su za suyi galaga* a cikin tsukin shekaru al'amura na Allah gabanin haka da bayan haka, a wannan rana musulmai za su yi farin ciki*(al—rum 1-4).

Manzo (s.a.w) ya ce : misalin muminai wurin san hunansu da tauyinsu da qaunan junansu, misali jiki ne idan gava xaya daga ciki ta sami rauni sai sauran gavovin jiki suyi rige rige wurin jin zafin da rashin barci." Buhari da Musulum suka ruwaito da wasunsu.

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Kungiyar mu’ujizar ilimi na Alqur’ani da Sunna da duniya  (1428-2007)