|
Haqiqar
ilimi:
Littafin farko da da ya bayyana a kan ilimin koguna da
tekuna a
qarni na sha
takwas babu bayanai masu gamsarwa na ilimi a ciki daga
baya ilimin tekuna ya
qara
samun bunqasa
lokacin da jirgin ruwan Ingila ta farko calengar ta fara
kewaya duniya daga shekara ta 1872 har zuwa 1876, sanna
kuma aka cigaba ta tafiye tafiyen ilimi don bincike
ruwa., a
qarshen
qarni na ashirin
aka
qara
samun masaniya kain da nain game da tekuna ta hanyar
amfani da tauraron
xan Adam da
xaukan
hoto daga nesa, bayan anyi waxan nan gwaje
gwajen da dama aka gano cewa: makwararan ruwan teku da
na koguna da koramai ko wanne yana da yana yinsa dabam
da kuma irin halittun da suke rayuwa a cikinsa duk da
cewa akwai cuxuwar
ruwa tsakaninsu da shigan juna, gwargwadon kwararan ko
wanne daga cikinsu da kai komon su, amma duk da haka
akwai shamaki tsakanin makwararan ko wanne da ga cikinsu
basa haxewa
da juna . kamar yadda aka gano cewa akwai wasu halittu
da basa rayuwa awasu nahiyoyin makwaran ruwa akwai inda
ma ba a samun wani abu mai rai a ciki, duk da ambaliyar
da ruwa ke yi atsakaninsu.saboda kowanne yanke bvantuwa
da irin suffofinsa. |
|
Fuskacin mu;ujiza:
Ko
wane taruwan ruwa za a iya kiranra kogi, amma ruwan daxi
mai garxi
sosai shine kogi, ruwan zartsi mai gishiri sosai shi ne
teku, ta haka zamu fidda makwararan ruwa wato mahaxa
ta yadda ba za mu iya kiransa da ruwan garxi
ba ba kuma zamu iya ce masa ruwan zartsi ba, don haka
muna da kashin ruwa har uku kenan ruwan garxi
da na zartsi da na tsaka tsaki.wanda aka sifata a cikin
Qur'ani cewa akwai
shamaki a tsakaninsu basa haxuwa
, wato ruwan garxi
ba zai rinjayi ruwan zartsi ba, wannan shi ne abin da ke
rabe magudana ruwa. Uku ko wanne da siffofinsa da
yanayinsa da kuma irin halittun da suke rayuwa ciki.
Tarihi ya tabbatar da cewa babu wani ilimi da ya shafi
ruwa mai zurfi a cikin shekaru 1400 da suka gabata, amma
duk da haka Alqur'ani
ya bayyana mana wannan abu cikin cikakken bayani mai
gamsarwa ta hanyar cakuxuwar
ruwa da koramai da koguna da teku, kuma ko wane na da
siffofinsa.
Ta
ina aka smi wannan bayanai b tare da tauraron dan ADAM
ba, ba kuma wasu kayan gwaje gwaje na takanolaji, indai
wannan bayani ba daga wurin Allah da yasan komai da
komai ba. |